Ambaliya Ruwa Da Iska Ya Jawo Asarar Rayuka Da Dukiya A Jihar Katsina

Al’ummar yankin Kukan Dan Maciji da ke karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina sun wayi gari cikin mummunan tashin hankali sakamakon iftila’in ruwan sama da iska mai karfi da aka yi a daren jiya Lahadi wanda ya janyo musu asarar rayuka masu yawa da kuma dimbin dukiya masu tarin yawa.
Ya zuwa yanzun dai da ake tattara wannan rahoton ba’a iya kididdige adadin rayuka da kuma gidajen da suka salwanta ba a sakamakon wannan iftila’i da ya afka wa al’ummar wannan yanki wadanda da yawa masu kananan karfi ne, ba su da ko dan abinda za su saka a bakinsu sakamakon rashin karfi da kuma yanayin halin rayuwa da ake ciki.

Post a Comment

0 Comments